Muna zaune ne a cikin irin 'yan kananan gidajen dogayen bene wanda yawancin mutane tsaka-tsaki ke zama. Amma, magunan da ke son zama a wajen har sun fi mutane yawa. Saboda wadannan dabbobi masu farata, yan uwa ga namun daji irinsu Zaki, Damisa da ire-irensu ba sa jin tsoron kowa. Wadannan halittu da akewa lakabin "mage mai rai tara" suna damun kowa amma kuma su na bada wani sauki ga mutane da dama.
Magunan da ke layin mu, kowacce ta san iya muhallinta. A hawa na kasa da benen farko da na biyu, magunan ba su cika fita daga inda su ke ba idan dai ba sun dan kewaya neman abinci a wasu madafu ba. A kan baranda yawanci kanana maguna ke zama idan ba tsoffin maguna da ke kwanciya suna ta lashe jiki ko shakar hantsi ba. Yawancin manyan magunan kuwa na labewa a lunguna inda ba za'a dame su ba su yi barci, wato kamar dakin maigadi inda zasu same shi yana barci. Allah ya yi wa maguna baiwa ta fitar da sauti na gurnani ko kuka, wasu daga cikin magunan a unguwarmu na hana mazauna wurin barci da kuka da guje-guje cikin dare.
Wasu mazaunan wurin da ke burin zama a tsaftace kamar magunan, na jin haushi a yayin da magunan su ka yi kaca-kaca da wuri. Hakika shahuna da ke yanki zasu so a ce an kori duk magunan amma kuma tattabaru na dako su ga ina mage zata yi tsalle, To, amma ba mu san wa zai zo ya kubutar da magunan ba.